Wayne Rooney ya ce a koda yaushe yana dokin buga wa Everton wasa a gasar Zakarun Turai ta Europa.
Everton za ta buga wasan cike gurbi da MFK Ruzomberok ta Slovakia a Goodison Park a yammacin Alhamis.
Rooney mai shekara 31, zai buga wa Everton karawar a karon farko tun bayan da ya bar kungiyar sama da shekara 13 ya koma Manchester United.
Ya koma United da taka-leda yana da shekara 18 kan kudi fan miliyan 27 a shekarar 2004.
Add Comment