Wasanni

Rooney ya koma Everton da taka-leda

Wayne Rooney Ya Koma Man. United a 2004 Akan Kudi Fan Miliyan 27

Wayne Rooney ya sake komawa Everton kungiyar da ya bari shekara 13 da suka wuce daga Mancherster United.

Rooney mai shekara 31 shi ne dan wasan da ya fi ci wa United kwallaye a tarihi, ya kuma koma Everton a matsayin wanda yarjejeniyarsa ta kare a Old Trafford.

 

Dan wasan ya ci wa United kwallo 253 a wasa 559 da ya buga mata tamaula.

Rooney ya ci kofin Premier biyar da na Zakarun Turai da na Europa da kofin Kalubale, tun komarsa United kan kudi fam miliyan 27 a shekarar 2004.

Tuni United ta amince ta dauki Romelu Lukaku daga Everton kan kudi fam miliyan 75.

 

Souce In BBCHAUSA