Romelu Lukaku ya ci kwallonsa ta farko a Manchester United a wani wasan sada zumunci inda kungiyar ta Jose Mourinho ta doke Real Salt Lake da ci 2-1 .
Dan asalin Beljium din mai shekara 24, wanda ya zo Manchester daga Everton kan Fam miliyan 75 ya ci kwallon da ya raba gardama a wasan, mintoci bakwai kafin a je hutun rabin lokaci bayan Henrikh Mkhitaryan ya ramawa United kwallon da aka zura mata a minti 20.
Daga baya United ta rasa Juan Mata da ya ji ciwo da kuma Antonio Valencia da aka ba wa jan kati.
Morinho ya ce : “[kwallon Lukaku] ya yi kyau, amman ba wani abu ne mai muhimmanci ba a gare ni.”
Kociyan na Manchester ya kara da cewa: “Na gaya masa ina kaunar abin da yake yi. Yana taimakawa a sha kwallo. Yana ja. Yana rike kwallo da kyau. Ina kaunar duk abin da yake yi.”
Mata ya fita daga filin da dingishi bayan Sebastian Saucedo ya taka shi, kuma ana tsammanin zai yi mako guda bai taka leda ba.
Daga baya kuma aka kori Valencia daga filin wasa sakamakon taka Saucedo da ya yi, lafari Allen Chapman ya yi magana da Mourinho kafin daga bisani ya kori dan asalin kasar Ecuador din.
Kociyan old Trafford din ya yi bayanin cewa: “An samu jikirin ne saboda lafarin ya nemi in sauya ‘yan wasan, kuma ni ban yi hakan ba saboda ban yarda da katin ba.”
Lukaku ya ci wa Everton kwallo 25 a gasar Firimiya a kakar bara.
Bbchausa
Add Comment