Rikicin Zamfara: Gwamnati na samun bayanan sirri


0 118

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Mai magana da yawun Shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya bayyana dalilin gwamnatin tarayya na dakatar da hakar ma’adinai a jihar Zamfara.

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samu bayanan sirri kan alakar da ke tsakanin hare-haren da ake kai wa a yankin da kuma hakar ma’adinan da ake yi.

Sai dai bai fito fili ya bayyana irin bayanan da gwamnatin ta samu ba game da alakar hakar ma’adinan da kuma barnar da ke faruwa a jihar ta Zamfara.

Amma ya bayyana cewa matakin da aka dauka na da alaka da matsaloliin da jihar ke fuskanta.

Ya ce ban da ‘yan Najeriya, akwai wadanda ba ‘yan kasa ba da dama da suke aikin hakar ma’adinai inda wasu ke yi bisa ka’ida wasu kuma ba su da lasisin yin hakan.

Garba Shehu ya bayyana cewa ya kamata jama’a su yi hakuri domin gwamnati na nan na bincike kuma jama’a za su samu gamsuwa da sakamakon da gwamnati za ta fitar.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Ya ce akwai hadakar rundunonin da aka kafa na sojojin kasa da na sama da sauran jami’an tsaro inda ya bayyana cewa an ba su umarnin yin maganin duk irin fitinar da ta kunno kai a fadin kasar.

Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnatin kasar na takaicin kara kunno kan irin wannan matsala ta rashin tsaro.

A ranar Lahadi ne gwamnatin kasar ta sanar da dakatar da hakkar ma’adinai a jihar Zamfara.

Sanarwar ta biyo bayan wata zanga-zanga da dubban ‘yan Najeriya suka yi ta matsa wa gwamnati da ta dauki mataki wajen kawo karshen hara-haren ‘yan bindiga a jihar ta Zamfara.

Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya jiha ce da ta yi kaurin suna wajen samun hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.

Tun a baya gwamnatin kasar ta sha aikawa da rundunonin sojojin sama da na kasa domin shawo kan matsalar, amma da rikicin ya lafa kwana biyu sai kuma ya kara barkewa.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.