DARA TA CI GIDA: Kimanin ‘Yan Boko Haram Da ‘Yan Kungiyar ISWAP 54 Ne Suka Mutu A Yayin Rikicin Da Ya Barke A Tsakaninsu
Daga Muhammad Kwairi Waziri
Kungiyar Boko Haram karkashin jagorancin Abubakar Shekau da na ISWAP sun yi mummunan rikici da juna kan mallakan wani yanki a Tafkin Chadi.
Kungiyar ta Boko Haram sun fara kai wa ISWAP harin ba-zata ne a ƙauyen Chikka.
Boko Haram sun mamaye kauyen inda suka kashe ‘yan kungiyar ISWAP da dama tare da sace matansu guda biyar, tare da sace musu kayayyakin abinci kafin su gudu a cikin dare.” kamar yadda Jaridar PRNigeria ta wallafa.
Daga baya kuma ISWAP ta kai harin ramuwar gayya inda suka yi barin wuta da ‘yan Boko Haram a yankin Kaduna Ruwa da Kaiga kuma an yi asarar rayuka daga bangarorin biyu, a cewar Jaridar PRNigeria.
Daga bisani kuma mayakan Boko Haram sun kashe wasu makiyaya 22 tare da sace shanunsu saboda sun biya haraji ga ISWAP a madadin ɓangaren Shekau.
Haka zalika sun afkawa wa wani kwalekwalen da ke dauke da makamai na ISWAP inda suka kashe mayaka takwas suka kwashe makaman da ke cikin kwalekwalen.
Kimanin mutane 54 ne dai daga bangarorin biyu ake zargin sun mutu a yayin rikicin.