Shugaban Hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati (EFCC), Ibrahim Magu, ya yi kira da a kafa kurkuku a dajin Sambisa domin a rika tsare wadanda suka aikata laifin cin hanci da rashawa a kasar.
Shugaban ya yi kiran ne a lokacin da ake bikin bude sabon ofishin shiyya na hukumar a Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Dajin Sambisa wata maboya ce ta mayakan Boko Haram a jihar Borno ta arewa maso gabashin kasar.
“Muna kira da a kafa wani kurkuku a dajin Sambisa domin kawar da masu laifukan cin hanci da rashawa daga cikinmu”, in ji Magu.
Har ila yau, ya yi kira ga bangaren shari’an kasar da ya mara wa kokarin gwamnatin tarayya wajen yaki da cin hanci da rashawa.
“Dole ne mu sauya lamarin ta hanyar yaki haikan da masu neman gurgunta nasarar da muka samu,” in ji Magu.
Ya ci gaba da cewa: “Kuma dole mu hada karfi wuri guda domin mu kashe cin hanci da rashawa kafin ya kashe mu.”
A karshe ya yaba wa gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufai domin taimakon da ya ba hukumar wajen bude ofishin shiyyar a jihar.
Souce in Bbchausa
Add Comment