Kannywood

Rigima Ta Barke Tsakanin Kannywood Da Shafin Northflix

Wata sabuwa rigima ta barke tsakanin shafin nan da yake sai da finafinan hausa mai suna Northflix da producers na fina finai.

Inda muka gano wani post da shahararren mai daukar nauyin finafinai wato Abdul Amart Maikwashewa yayi a shafinsa na Instagram inda yake cewa:-

Bamuyi tunanin zamuyi danasani da yin hulla dakuba amma sai gashi kun zama MACUTA agaremu, mun baku kayanmu (films) da niyyar kasuwanci amma sai harkar takoma zabba cikin aminci, kun mayar da kayanmu kamar wanda kuka gada, kunje kuna sarrafa kayanmu da yadashi ta yadda kukaso, @northfilix kun zama azzalumai macuta wadanda bakwason cigaban kannywood, kuma ko sauraremu don akwai mataki nagaba…
Reposted from @abdulamart_mai_kwashewa

Inda akasan post nasa mukaga ra’ayin shararren mai daukar nauyi Bashir Maishadda yana cewa:

Wallahi nima sun zalinceni, Wallahi bazan yarda ba.

Daga bisani kuma sai gashi wani mai kallo a wannan kafa shima ya bayyana ra’ayinsa inda yake cewa

Alhmdllh ashe ba mu ƴan kallo kadai suke cuta ba har daku masu abin kallo.
Allah zai saka mana dukkanmu.

Cire mana kudi sukeyi ba tare da consent dinmu ba monthly, sannan basu da wasu films da suke sawa a kasrhe naje na cire ATM card dina, ai ba dole bane kallon

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: