Wasanni

Real Madrid Za Ta Yi Wa Isco Kora Da Hali

Wasu rahotanni daga kasar Sipaniya suna nuni da cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ba za ta bai wa dan wasanta na tsakiya Isco sabon kwantiragi a kungiyar ba saboda wasu dalilai wadanda ba’a bayyana ba.

Dan wasan mai shekaru 29 na daf da zama babu wata igiyar yarjejeniya a kansa, inda a shekarar 2022 ne kwantiraginsa zai kare, kuma yana da damar barin Santiago Bernabeu a wannan bazara, duk da cewa Carlo Ancelotti ya dawo a kungiyar a karo na biyu a matsayin mai horarwa.

Gaba daya sau goma ne kawai aka fara wasa da dan wasa Isco a dukkan gasanni a lokacin mai horarwa, Zinadine Zidane a kakar wasa ta shekarar 2020 zuwa 2021, kuma ana danganta shi da komawa gasar Firimiyar Ingila.

Sai dai ana ganin zuwan Ancelotti bai canza komai ba a game da abin da Isco ke fuskanta a Real Madrid ko kadan domin kungiyar na ta kokarin sayar da dan wasan da ya taho daga Malaga domin kauce wa yanayin da zai sa ya bar kungiyar ba tare da ta samu ko sisin kwabo ba a lokacin da kwantiraginsa zai kare a shekarar 2022.

Real Madrid ta rabu da dan wasa kuma kaftin din kungiyar, Sergio Ramos wanda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German sannan kuma tana shirin sayar da Rafael Varane ga kungiyar Manchester United a wannan satin.

A kwanakin baya kungiyoyin Tottenham da Jubentus da wasu daga cikin kungiyoyin firimiyar Ingila sunyi yunkurin sayan dan wasan sai dai Real Madrid ta dage akan cewa ba zata sayar dashi ba.

Isco ya taimakawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe kofunan zakarun turai guda hudu da gasar La liga guda uku sannan kuma ya lashe kofin nahiyar turai da tawagar ‘yan wasan kasar Sipaniya.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement