Wasanni

Real Madrid Za Ta Fara Gina Sabuwar Tawaga Da Camavinga

Bayan tayin kudi har sau biyu da Real Madrid ta yi wajen sayan dan wasa Kyian Mbappe daga kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German, Real Madrid ta fara sayan matasan ‘yan wasan da za ta gina sabuwar kungiyar.

Kungiyar ta kammala daukar dan kkwallon tawagar Faransa, Eduardo Camavinga daga Rennes kan yarjejeniyar kakar wasa biyar kuma dan wasan mai shekara 18 yana cikin kwantiragin karshe a kungiyar da ke buga Ligue 1, wadda ta sayar da shi in ba haka ba zai yi zaman mara yarjejeniya da kungiyar.

Ranar Litinin aka auna koshin lafiyar dan kwallo a Faransa a wajen atisaye na Clairefontaine kuma a watan Afirilun shekara ta 2019Camavinga ya zama matashin dan wasan Rennes da ya fara buga mata wasa yana da shekara 16 da haihuwa da wata hudu a lokacin kuma cikin kakar wasa biyun da ya yi a kungiyar Camavinga ya buga mata wasanni 60.

Matashin ya zama mai karancin shekaru da ya buga wa tawagar Faransa wasa a karawa da Croatia a Nations League a watan Satumbar shekara ta 2020, sannan ya kuma fara ci wa Faransa wasa wata daya tsakani a wasan sada
zumunta da Ukraine da ta yi nasara da ci 7 1.

Bayan da Faransa ba ta gayyace shi gasar Euro 2020 ba, ya wakilci kasar a gasar cin kofin nahiyar Turai ta matasa ‘yan kasa da shekara 21 a bana kuma Camavinga shi ne na biyu da Real Madrid ta dauka, bayan David Alaba wanda ya koma Sifaniya da buga wasa daga Bayern Munich.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement