Wasanni

Real Madrid Za Ta Buga Wasanni Shida A Watan Satumba

A karshen makon nan za a ci gaba da wasannin gasar kasashen Turai, inda Real Madrid za ta yi karawa shida a cikin watan kuma cikin fafatawar da za ta yi biyu daga ciki a Champions League za ta kara da Inter Milan da kuma FC Sheriff Trispol ta Rasha.

Sauran wasanni hudu kuwa a La Liga za ta yi da ya hada da kungiyoyin Celta Bigo da Balencia da Mallorca da kuma Billareal kamar yadda hukumar kwallon kafa ta kasar Sipaniya ta tsara.

Real Madrid wadda ta yi wasanni uku a kakar bana a La Liga ta je ta doke Real Betis 1-0 ranar Asabar 28 ga watan Agusta, sai dai kafin wannan wasan na Real Betis Real Madrid ta fara buga gasar La Liga ta bana da cin Alabes 4-1 ranar Asabar 14 ga watan Agusta, sannan ta tashi 3-3 a gidan Lebante ranar Lahadi 22 ga watan Agusta.

Real Madrid wadda ta buga wasanni uku a bana a La Liga a waje, za ta karbi bakuncin Celta Bigo ranar Lahadi 12 ga watan Satumba, lokacin dukkan ‘yan wasa sun koma kungiyoyinsu bayan buga wa kasashensu wasannin shiga gasar kofin duniya.

Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki bakwai, bayan wasanni uku, sauran masu maki bakwai-bakwai sun hada da Sevilla da Balencia da Barcelona da kuma Atletico Madrid mai rike da kofin a bara.

Ga Jerin Wasa Shida Da Real Madrid Za Ta Fafata Cikin Watan Satumba:

Gasar La Liga a ranar Lahadi, 12 ga watan Satumba

Real Madrid da Celta Bigo

Champions League a ranar Laraba, 15 ga watan Satumba

Inter Milan da Real Madrid

Gasar La Liga a ranar Lahadi 19 ga watan Satumba

Balencia da Real Madrid

Gasar La Liga na ranar Laraba, 22 ga watan Satumba

Real Madrid da Mallorca

Gasar La Liga a ranar Asabar, 25 ga watan Satumba

Real Madrid da Billarreal

Champions League a ranar Talata, 28 ga watan Satumba

Real Madrid da FC Sheriff

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement