Wasanni

Real Madrid Tana Neman Dan Wasan Manaco

Har yanzu dai Real Madrid ba ta dauki wani dan wasa mai tsada sosai ba tun bayan bude kasuwar musayar ‘yan kwallo ta Turai.

 

Sai dai an ta rade-radin cewa Madrid din na zawarcin dan wasan Monaco Kylian Mbappe da Pierre-Emerick Aubameyang na Borussia Dortmund.

Amma dai har yanzu babu wani labari game da wannan batu.