Real Madrid Ta Shiga Neman Dan Wasan Da Chelsea Da Liverpool Ke Nema

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Rahotanni daga kasar Italiya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real madarid ta shiga zawarcin dan wasan kungiyar kwallon kafa ta AC Millan, Suso domin yakoma kungiyar a watan Janairu. Kungiyoyin Liberpool da Chelsea ne dai suke zawarcin dan wasan wanda a baya ya taba bagawa kungiyar kwallon kafa ta Liberpool wasa lokacin da yana matashin dan wasa kafin kungiyar ta siyar da shi. Kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ce dai ta siyar da dan wasan ga AC Millan kuma kawo yanzu ya kasance daya daga cikin manyan ‘yan wasan da kungiyar ta kasar Italiya take ji dasu a duniya. Suso dai shine kawo yanzu yafi kowanne dan wasa taimakawa a zura kwallo a raga a wannan kakar a duka gasannin nahiyar turai bayan daya taimaka aka zura kwallaye bakwai a raga a wannan kakar a kungiyarsa ta Milan.

Wasu Abubuwan Masu Alaka

[Music] B Zango -Tausayamin

1 of 54

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dai tana ganin zata iya samun dan wasan wanda aka yiwa kudi kusan fam miliyan 25 kuma kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ma ta shirya biyan kudin idan har ya amince zai koma kungiyar. Real Madrid dai tana neman dan wasa matashi wanda tauraruwarsa zata haska anan gaba kuma mai saukin kudi domin tayi amfani da kudin da take dashi wajen siyan ‘yan wasa Edin Hazard ko Kylian Mbappe ko Neymar.

 

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: