Labarai

Real Madrid ta kara wa Zidane kwantaragin shekara uku

Mai horas da ‘yan wasan kwallon kafa na kungiyar Real Madrid, Zinadine Zidane ya kara sa hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar ci gaba da koyar da wasa har zuwa 2020.

 

Zidane ya sa hannun ne kwana uku bayan ya yi nasarar cin kofin Gwarzayen Zakarun Turai, inda kungiyar sa ta lallasa Manchester United da ci 2:1.

Da ya ke jawabi Jim kadan bayan ya sa hannu, Zidane wanda kwararren tsohon dan wasan kungiyar ne, ya samu nasarar cin kofin La Liga da kuma Champions League na kakar wasannin 2016/2017.

Ya yi gamo-da-katarin nasara a Real Madrid tun bayan da ya maye gurbin Barnitez cikin watan Janairu, 2016, inda ya samu nasarar lashe kofin Champions League na 2016, watanni biyar bayan damka masa ragamar koyar da ‘yan wasan Real Madrid.

A jawabin nasa, ya ce abin alfahari ne a gare shi a ce shi ne mai koyar da kasaitaccen kulob kamar Real Madrid. Sai ya sha alwashin kara lashe wasu gasar da ke gaba.

“Wannan koyar da wasa kalubale ne a gare ni, kuma abin dubawa ba wai yawan shekaru ka na koyar da wasa ba ne. Wace nasara ka yi? Shi ne magana. Don haka muddin za ka yi nasarar abin da ka sa a gaba, to da shekara goma ko shekara uku duk daya ne.

Zidane dai ya kasance mai horas da ‘yan wasan da kungiyar Real Madrid ke dasawa da shi.

An zuba ido a ga irin rawar da zai taka a wannan kakar wasanni.

Real Madrid ta buga wasanni 68 a jere ba tare da ta yi fashin jefa kwallo ba, ko da guda daya ne, a karkashin Zidane.

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.