Labarai

Rayuwar Ragowar Wadanda Harin Jirgin Kasan Kaduna Ya Rutsa Da Su Na Cikin

Bidiyo: Rayuwar ragowar waɗanda harin jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja ya rutsa da su na cikin haɗari yayin da ISWAP ke barazanar sayar da su, da yanka su.

 

 

Wannan shi ne karo na karshe da za mu bukaci gwamnati ta yi Abinda ya dace don ganin an ‘yanto su kafin mu sayar da ko mu yanka su, da yardar Allah za mu kawo masu rike da madafun iko da suka hada da shugaban kasa, Gwamna Nasiru El-Rufai, Sanatoci da sauran azzalumai kamar yadda muka kawo wadannan mutanen gabanmu.

 

 

Kungiyar Islamic State of West Africa Province (ISWAP) ta dauki alhakin harin da aka kai kan jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna.

 

A cikin wani faifan bidiyo na mintuna 10 da wannan kafar yada labarai ta Samu, masu garkuwa da mutanen anga suna dukan wadanda abin ya shafa ba tare da tausayin su ba, sunq baiwa gwamnatin tarayya umarnin da ta kawo musu dauki kafin a makara.

 

 

Wasu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su da suka yi magana sun zargi gwamnatin tarayya da yi wa rayuwar ‘yan kasarta rikon sakainar kashi inda suka ce da jami’an gwamnatin za su dauki wani mataki na daban idan ‘ya’yansu ko ‘yan uwansu ke da hannu a lamarin.

 

Kazalika sun zargi gwamnatin kasar da kawo cikas ga kokarin ‘yan uwansu na ceto su daga hannun ‘yan ta’addan.

 

“Me muka yi da muka cancanci wannan cin zarafi? Shin ya zama laifi idan mutum ya zama dan Najeriya? Yanzu kimanin watanni hudu da suka wuce kuma gwamnati ba ta dauki wani kwakkwaran mataki na ceto mu ba hakan yana nufin rayuwarmu babu.

 

 

“’Yan uwanmu sun yi kokarin kubutar da mu daga hannun wadanda suka yi garkuwa da mu amma a dajin karshe sojoji sun hana su zuwa domin neman belin mu.

 

“Tunda gwamnatin tarayya ba ta damu da rayuwarmu ba, muna kira ga kasashen duniya da su kawo mana dauki domin rayuwar mu ta tabbata.” Inji su.

 

A cikin faifan bidiyon, wani mutum a cikin kayan soji wanda ya yi ikirarin cewa yana daya daga cikin fursunonin Kuje da aka ceto.

 

Ya kara da cewa tunda gwamnatin tarayya ta kasa sakin shi, Allah zai yi amfani da shi wajen kawo wa dukkan wadannan azzaluman abin kunya irin wanda ya faru da fasinjojin jirgin.

 

A baya-bayan nan dai an sako fasinjojin jirgin kasa guda 11 da 7 da aka sace sakamakon kokarin da mawallafin jaridar Kaduna, Tukur Mamu ya yi wanda ya yi alkawarin ba zai taba shiga aikin ceto ba saboda rashin bada hadin kai da gwamnatin tarayya ta yi.

About the author

Sulfidone

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement