Muhawara

RAYUWAN MATA MASU DOGON BURI AKAN AURE!

RAYUWAN MATA MASU DOGON BURI AKAN AURE!
Magana tsakanin kawa da kawa.
Age15——-kawa yaushe zakiyi aure ne? Hmmm wani aure kuma yanzu, sai nagama secondary school, nayi University kafin nayi aure.
Age18———kawa ya labarin aure? Hmmm so nake idan ko nakai 200level sai nayi.
Age20———kawa ya maganar aure ne? Hmmm tohhh inda so samu ne ina graduating idan Allah yakawo miji sai nayi aure.
Age23——–kawa kinki aure ko!!! Hmmm Aure lokaci ne, lokacinshi ne baizo ba.
Age25——–kawa kinji Amina ta haihu ko!! Toh Allah yaraya, nikam tohhh mazan ne duk wanda kace ya turo sai yagudu.
Age27———kawa ke kam haryanzu kinacin zamaninki!!! Hmm banson wulakanci, kibarni da abunda ke damuna ni yanzu ko mai wanki da guga ne Allah yakawo mun zan aura.
Age30——-kawa ke kam haryanzu ba labari!! Hmmm ai ina ganin saurayin DELU kawai zan kwace saidai komi zaifaru yafaru.
Age33——–kawa nazomiki da wani shawara meyasa bazaki kawo hotonki akai babban Masallaci ba ko za’adace!!! Toh shikenan.
Age35——-kawa lokaci yanata kurewa, akwai wani malami ko zamuje wurinsa ne? Toh indai aikinsa yanayi muje kawai.
MATA SAI KU KULA!!!
Rubutawa :
Haiman Khan Raees 
@HaimanRaees