Masu ba da umarni a Kannywood sun ce harkar ta na bunkasa ne sakamakon horo da suke samu.
A bana ne ake cika shekaru 20 da fara harkar fina-finan Hausa, wacce aka fi sani da Kannywood.
Harkar dai ta fuskanci fadi-tashi daban-daban har ta kawo matsayin da take a yanzu.
Masu ba da umarni a Kannywood din sun ce harkar ta na bunkasa ne sakamakon horo da suke samu da kuma bincike da suke kara zurfafawa a harkar fina-finan.
Wani mai ba da umarni Yasin Auwal wanda shi ne ya ba da umarni a fim din da aka zabi Sadik Sani Sadik a matsayin gwarzon jaruman fina-finan Hausa na bana, ya ce sune kashin bayan duk wata nasara da ake samu a harkar.
Add Comment