Jihar Bauchi ta shiga jerin jihohin da suka yi zarra a bangaren kula da kiwon lafiya. Jihar ta shiga jerin jihohin da aka gayyata a shirin bunkasa kiwon lafiya karo na Biyu da ya gudana a fadar shugaban kasa.
Shirin mai taken “Saving of One Million Lives Programme for Results (SOML – PforR)” nada kudurin ganin akalla miliyoyin yan Nigeria sun amfana da tallafin kula da ingantacciyar kiwon lafiya daga 2018 zuwa 2022.
Gwamnan jihar Bauchi, MA Abubakar ne ya wakikci jihar. Sauran Gwamnoni 5 da suka samu halartar taron akwai Gwamnonin jihohin Kano, da Borno, da Ondo, Ekiti da kuma Edo, sauran sun hada da mataimakan Gwamnonin jihohin; Niger, da Benue, da Yobe da kuma Jigawa.
Hadimin Gwamnan Bauchi a fannin sadarwa, Shamsudeen Abubakar ya yiwa Hausa Times karin bayani da cewa “muna yiwa Allah godiya da yasa duniya ma ta shaida irin yadda jihar mu ta samu sauyi a fannin kiwon lafiya.
- Advertisement -
Wannan hobbasar kuma ta samu asali ne sakamakon jajircewar maigirma Gwamna da taimakon mai dakinsa wacce kowa ya shaida gudunmuwar da take bayarwa wajen ganin an samu biyan bukata musamman a fannin kiwon lafiya wacce akeyiwa lakani da lafiyar uwar jiki sai kuma hadiman mai girma Gwamnan daga Kwamishina zuwa sauransu”
Ba shakka Gwamnatin jihar Bauchi na taka muhimmiyar rawa a bangaren kiwon lafiya. Ko a kwanakin baya sai da uwargidan Gwamnan jihar Hajiya Hadiza ta kaddamar da asibitoci da aka gyara aka sanya kayayyakin aiki.
Masu hasashen siyasa dai na ganin muddin Gwamnan ya cigaba da mulkar jihar to babu shakka akwai yiwuwar Bauchi ta yiwa jihohin kasar fincinkau.