Uncategorized

Rashin wuta ya ta'azzara a Nigeria

Matsalar rashin wuta na kara ta’azzara a Najeiya
Matsalar karancin wutar lantarkin da ake fama da ita a Nigeria tun ranar Talata ta kara ta’azzara a ranar Alhamis, inda aka rasa wutar da za a raba kwata-kwata a wasu sassan kasar.
Wani bayani da ya fitowa daga wata majiya a kamfanin rarraba wutar lantarki na babban birnin tarayya Abuja, AEDC, ya ce da misalin karfe 1 na ranar Alhamis bai sami wuta ko da megawat daya da zai rabawa mazauna birnin da kewaye ba.
Kamfanin ya ce tun da fari babban kamfanin da ke tura wuta ga kamfanonin da suke rabawa ya ce zai samar musu da megawat 257.97 a ranar Alhamis, amma sai gashi ko megawat daya kamfanin AEDC bai tsira da shi ba. 
Kamfanin rarraba wutar na Abuja ya ce bai san yadda zai samu wutar da zai rabawa al’ummar birnin ba.
Sai dai mai magana da yawun kamfanin Seun Olagunju, ta ce matsalar na’ura ce suka samu kuma <span >injiniyoyinsu na aiki don shawo kan matsalar.
Ta kara da cewa <span >kashi 20 cikin 100 aka basu, kuma suna sa ran zuwa tsakar dare za su samu kashi 80
<span >Ana dai fama da matsanancin karancin wutar lantarki a Najeriya inda ake raba megawat 2,243.20 ga dukkan jihohin kasar.