Labarai

Rashin lafiyan Buhari: Abun da Allah ya sanar dani game da shugaban kasa – Fasto Kasali

-Shugaban kasa yagama aikin sa a Najeriya tun farkon shekaran nan

-Zunuban mu shi ya janyo mana matsalolin da mu ke ciki

-Buhari mutumin kirki ne amma shaidan ya kama kasannan

Shugabam cocin, Mercy Prayer Ministry worldwide dake Ibadan Jihar Oyo.

Fasto Muyideen Kasali yace laifufukan da yan Najeriya kai yi wa Allah shi ya sa shugaban kasa ya kasa magance matsalolinn kasan.

Yace Buhari ya ga ma aikin sa a Najeriya Mallamin cocin yace ya samu wahayi daga Allah cewa Buhari yagama aikin sa a Najeriya tun farkon shekaran nan.

 

Faston wanda makaho ne yace idan muna son Allah ya magance mana matsalolin mu a kasannan dole koma ga Allah.

Manufofin shugaban kasa ma kasannan masu kyau ne, amma zunuban mu kai janyo mana matsalolin da mu ke fuskanta, duk da rashin lafiya Buhari da zai iya magance matsalolin Najeriya amma nauyin laifufukan mu shi ke hana mu samun nasara inji faston.

Ya kuma gargadi wanda suke son raba kasannan da cewa Allah ne yahadu mu, shi yasan dalilin da yasa yayi haka kuma shi zai magance matsalolin da muke fuskanta kuma muna adu’a Allah ya hada kawunan yan Najeriya saboda duk wajen da akwai soyayya, nan rahaman Allah yake.