-Advertisement-


Rashin Ilimi Ne Yasa Harkar Fim Ta Mutu – Salisu Mariri


0 432

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daya daga cikin matasan Jarumai kuma mai shirya fina-finai a masana’antar Kannywood, Salisu Nuhu Mariri, ya bayyana yanayin da harkar fim ta ke ciki a halin yanzu da cewa karancin ilimi da masu gudanar da harkar su ke da shi ne ya kai masana’antar ga halin da ta ke ciki a halin yanzu.

Jarumin wanda ya dade a na damawa da shi a cikin harkar, sama da shekaru goma sha biyar (15), sannan baya ga haka ya na cin tudu uku ne a masana’antar, domin kuwa shi jarumi ne, mashiryin fim ne kuma mawaki ne, wanda ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar sa da majiyar mu ta Northflix .

Ya kuma fara da cewa “Shigowa kai tsaye da mutane su ke yi cikin harkar ba tare da an bincika an san daga ina su ka fito ba, ya kawo babban matsala a cikin masana’antar, domin haka ne ya sa ba a ganin girman manya, kuma hakan sai ya zama babu wanda ya isa ya tsawatar idan a na yi ba daidai ba. Hakan ya sa mutuncin masana’antar kullum ya ke zubewa, saboda babu mai fada a ji, komai girman mutum idan ya yi magana, sai ka ga yaro karami a cikin mu ya zo ya na yi masa rashin kunya. Kuma babu wani abu da ‘yan fim su ka sa a gaba sai neman laifin juna da tona wa juna asiri, sannan duk wanda ya ke ganin ya daukaka, to ba ya son wani ya taso, sai ya rinka ganin babu wani sai shi, ya manta da cewa daukaka ta Allah ce kuma zai iya baiwa kowa”. Inji Salisu Mariri.

Ya ci gaba da cewa” A harkar fim babu wani mai girma sai masu kudi da kuma jaruman da a ke ya yi, amma duk wata basira ta ka idan ba ka da kudi ko ba a yayin ka sai a ke kallon ka kamar mara amfani, sai dai kawai a rinka bi ta bayan gida a na lallabar ka a na amfani da basirar ka, kuma ba za a nuna kai ne ka yi abun ba, domin idan a ka fada za ka daukaka. To Irin wannan halayen nan ne ya haifar da rashin hadin kai da taimaka wa juna, domin har yanzu babu wata kungiya a cikin Yan fim da ta ke taimaka wa magabatan a harkar da su ka bada gudummawa wajen samuwar ta duk da har yanzu akwai wandada su na nan da ran su, kuma su na bukatar taimako”. Inji Salisu Mariri.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 317

-Advertisement-

Mun tambaye shi ko me ne ne mafita dangane da wannan halin da ‘yan fim su ke ciki a yanzu?

Sai ya rufe da cewar “To gaskiya abun ya na bukatar nazari, kuma nazari mai kyau sai da ilimi a ke yin sa, domin ka ga a harkar nan mu na da karancin ilimi, kuma ita ce babbar matsalar da sai an magance ta sannan komai zai ta fi daidai, domin tun farko da kamar an gina harkar fim din Hausa a doron ilimi, to da tuni harkar ta wuce yadda ta ke a yanzu, amma saboda babu ilimi, kuma kowa ya shigo da bukatar sa ta sha’awa da kuma burin tara abun duniya, shi ya sa komai za ka iya samu a cikin harkar, domin wasu ko da za a yi gyaran to ba za su so ba, domin idan harkar ta gyaru to ba za su samu abun da su ke samu ba”. A cewar Salisu Mariri.

DAGA karshe ya yi kira ga masu harkar fim da su yi kokarin hada kan su tare da tashi tsaye wajen neman ilimi, domin su ceto masana’antar daga halin da ta samu kanta a ciki

#Northflix

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.