Kannywood

Rashin Aure Ma Azaba Ne, Inji Princess Ummi Ibrahim

Wata budurwa ƴar asalin jihar Borno da ke Arewacin Najeriya mai amfani da shafukan sadarwa musamman Facebook, Princess Ummi Ibrahim wacce aka fi sani da Gumsu ta bayyana cewa rashin aure azaba ce.

Ummi Ibrahim ta bayyana hakan a shafinta na Facebook, inda hakan ya tayar da ƙura tare kafsa muhawara a tsakanin waɗanda su ke bibiyar shafinta.

“Rashin Aure Ma Azaba Ne” Kamar yadda ta wallafa.

Sai dai kuma Princess Ummi ɗin ta sake yin wani wallafar rubutu inda a ciki ta ke shawartar maza akan su daure su ƙara aure, su kuma mata su yi haƙuri wajen zama da kishiya.

“Maza A Cire Tsoro A Kara Aure, Mata a Cire Kishi a Yiwa Amarya Oyoyo, Ciwon Ƴa Mace Na Ƴa Mace Ne” Inji Princess Ummi

Menene ra’ayinku akan wannan batu?.

-Idon Mikiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: