Labarai

Rashin albashi ya 'jefa' ma'aikatan Katsina cikin garari

Wasu ma’aikatan jihar Katsina da ke Najeriya sun ce an kwashe sama da wata 11 ba a biya su albashi ba, lamarin da a cewar su ya jefa su cikin mawuyacin hali.
Wasu daga cikin ma’aikatan sun shaida wa BBC cewa an hana su albashinsu ne bayan an yi karyar cewa ba sa zuwa aiki, suna masu cewa wasu manyan jami’an gwamnatin ne suka shafa musu kashin-kaji saboda sun san cewa su [ma’aikatan] sun fi manyansu kwarewa wurin aiki.
Sai dai gwamnatin jihar ta ce ta dakatar da biyan albashin ma’aikatan ne sakamakon zargin su da laifin kin zuwa aiki.
BBC ta gano cewa ma’aikata 792 aka hana albashi bayan an gano ba sa zuwa aiki.
Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, Alhaji Abdulkadir Ahmed Zakka, ya shaida wa BBC cewa an mayar da mutum 689 a bakin aikinsu bayan da aka gama bincike, yana mai cewa sauran ma’aikatan da lamarin ya shafa na bogi ne.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.