Labarai

Ranar Da Za’a Gudanar Da Bikin Dan Buhari Da Yar Sarkin Bichi

Za A Gudanar Da Bikin Auren Gimbiya Da Ɗan Shugaban Ƙasa Yusuf Muhammad Buhari, A Ranar 20 Ga Watan Agusta, Tare Da Naɗin Sarauta A 21 Ga Watan

Daga Zaharaddeen Gandu

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Jimillar mutane 145 aka sanya a cikin kwamitin da aka kaddamar domin tsara yadda za a yi bikin auren diyar Sarkin Bichi Zahra Ado-Bayero da ɗan Shugaba Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari.

Kwamitin, wanda Sarki, Nasiru Ado Bayero ya kafa, zai kuma shirya jadawalin naɗin sarautar, da kuma gabatar da ma’aikatan ofis da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje.

Masarautar ta fitar da sanarwa, mai ɗauke da sa-hannun kakakinta Lurwan Malikawa, tuni jadawalin ya fita.

Dangane da jadawalin, za a gudanar da bikin auren gimbiya da ɗan shugaban ƙasar, a ranar 20 ga watan Agusta, kuma naɗin sarautar ya biyo bayan kwana ɗaya a ranar 21 ga watan Agusta, a fadar Sarkin Kano.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, “kwamitin da aka kaddamar zai kasance ƙarkashin Hakimin Bagwai, wanda kuma shi ne Madakin Bichi Alhaji Nura Ahmad, da Falakin Bichi Alhaji Abba Waziri za su yi aiki a matsayin sakataren kwamitin”.

Ya kara bayyana cewa, “yayin bikin ƙaddamar da kwamitin, Sarkin Bichi, wanda Madakin Bichi ya wakilta, ya buƙaci mambobin kwamitin da su yi amfani da ƙwarewar da suke da ita wajen tabbatar da nasarar nadin sarautar da kuma na bikin auren sarautar”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: