Daga Ibrahim Baba Suleiman
Gwamnatin Saudiyya ta bada shelar cewa ba’a ga jinjirin watan Dhul-Hijjah a ƙasar ranar Litinin ba kamar yadda ake tsamnanin sa a lissafin kalandar ƙasar, Saboda haka yau Talata zai zama 30 ga watan zul-qaada, Arafah zai zama ranar Alhamis 31 ga watan Agusta, kana ranar Juma’a ita ce ranar Sallar laiya a kasar Saudiyya.
Kazalika a Nijeriya yau Talata shine 29 ga watan Dhul-Qadah a lissafin ganin watan ƙasar, kuma yau ne Sarkin musulmin ƙasar, Muhammad Abubakar Sa’ad III ya bada shelar fara duba jinjirin wata a faɗin ƙasar, da fatan in an gani za’a sanar da mahukunta har ya kai ga Sarkin Musulmi.
Allah yasa mu dace.
“Souce In Rariya”
Add Comment