Rakitic Yace A Barcelona Zaiyi Ritaya A Ball


2 1,883

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Iban Rakitic, ya bayyana cewa babu dalilin da zaisa yabar kungiyar tasa a halin yanzu domin komawa wata kungiyar daban kuma yace yana fatan cigaba da zama a Barcelona nan da wasu shekaru inda yace yana saran yin ritaya a kungiyar Tun a kwanakin baya aka fara rade radin cewa dan wasan dan asalin kasar Crotia zai bar kungiyar zuwa Manchester United sakamakon Barcelona ta siyi dan wasa De Jong daga Ajad dan kasar Holland.

Sai dai kamar yadda kasuwar siye da siyar da ‘yan wasa take sake kusantowa dan wasan ya bayyana cewa baya tunanin barin Barcelona a yanzu kuma yana fatan cigaba da zama nan da shekaru masu yawa.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 54

- Advertisement -

“Banason kasancewa a kowacce kungiya sai Barcelona anan gaba saboda babu inda zanje wanda yafi nan saboda haka ina fatan magoya baya da kociyan kungiyar da shugabanni suna irin tunanin da nakeyi kuma ina fatan zanyi ritaya anan” In Ji Rakitic wanda ya koma Barcelona daga Sebilla Yaci gaba da cewa

“Ina fatan zasu gayamin cewa zan cigaba da kasancewa anan har in gama kwallo na saboda babban burina shine kasancewa da wannan babbar kungiya kuma inada ragowar kwantaragi na shekara uku saboda haka babu inda zanje”

Rakitic dai ya buga wasanni 51 a Barcelona a wannan kakar kuma ya buga minti 90 a wasan da sukayi rashin nasara a hannun kungiyar Valencia a wasan karshe na cin kofin Copa Del Rey da suka fafata a ranar Asabar.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.