Fitaccen jarumin fina-finan Hausa a Najeriya, Adam A Zango, ya ce rarrabuwar kawunan ‘yan fim ce tasa al’umma ke yawan zaginsu har ma hakan ya jawo suke rasa abubuwa na cigaba a sana’arsu.
Adam Zango ya yi wannan tsokaci ne a shafinsa na Instagram, a wani martani da yake mayarwa kan janye gina dandalin shirya fina-finai da gwamnatin kasar ta so yi a Kano.
Adam Zango dai na ganin kiyayyar da ake wa ‘yan fim ce saboda halayen wasunsu tasa al’umma ta yi Allah-wa-dai da gina wannan masana’anta ta fim a jihar Kano, wadda da ta tabbata, ba karamin cigaba za ta kawowa harkar ba.
Zango ya ce, ”Idan an bi ta barawo a bi ta ma bi sawu. In har mu ‘yan fim ba mu daina yi wa juna hassada da butulci da rashin girmama na gaba ba, tare da gyara yadda muke tsara fina-finanmu to tabbas ba za mu tsira daga zagin al’umma ba.”
Ya kara da cewa dukkan ‘yan fim sun san bata-garin cikinsu masu jawo musu zagi.
”Mu yi iya kokarinmu wajan gyara masana’antarmu mu bar wa Allah sauran,” in ji Zango.
Sai dai kuma dan wasan ya yi kira ga jama’a da su daina yi musu kudin goro wajen kushe su.
- An soke shirin gina dandalin fim a Kano
- An yi raddi kan soke dandalin fim a Kano
- Yadda shafukan zumunta suka hana dandalin fim a Kano
Ya ce, ”Na tabbata akwai fina-finai da wakokin da muka yi domin mu bai wa addini da al’adarmu gudunmowa, amma babu wata kungiyar malamai da suka taba gayyatar daya daga cikinmu ta karramashi, sai dai da zarar mun yi kuskure sai a hau zagin mu ana kafirta mu.”
A don haka ya yi kira ga malamai da sarakun da gwamnati da su ja ‘yan fim a jiki don su ma ‘ya’yansu ne, ta haka ne za a samu fahimta.
Souce Code In BBchausa
Add Comment