Get New DJ Mixes
Labarai

A raba aure na da mata na don ta cika masifa

Wani magidanci Daniel Ezekiel ya sanar wa kotu cewa mai dakinsa ta kore shi daga gidansu da suke zama babu gaira babu dalili.

Ya ce haka kawai wata rana matarsa ta kwace mukullin motarsa ta kulle gidan sannan ta ce ya kama gaban sa.

“ shekara uku Kenan ina fama da hawa motan haya da biyan kudin hayar gidan da na kama.”

Matata ta cika masifa, bayan ni, bata bar makwabta ba, kullum kaji ta cikin hayaniya da mutane.

 

Ya roki Kotu da ta warware wannan aure nasu.

Matar tasa roki kotu da ta sassauta akan bukatar mijin nata.

“ Don Allah kada Kotu ta warware auren domin ina matukar son mijina. A dan bamu lokaci mu koma gida mu sasanta.”

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.