Dan wasan Barcelona Neymar ya amince da kwantiragin shekara biyar da kulob din Paris St-Germain inda suka ce za su saye shi a kan Yuro miliyan 220 a cikin mako mai zuwa, kamar yadda jaridar Metro ta bayyana.
Haka kuma PSG za ta bayar da tsohon dan wasan Manchester United Angel di Maria a cikin yarjejeniyar don ta samu kudin biyan harajin sayen Neymar, kamar yadda kafar yada labarai ta AS ta bayyana.
Idan Neymar ya bar Barcelona, kungiyar za ta maye gurbinsa da daya daga cikin ‘yan wasa uku da ke murza-leda a Ingila – Philippe Coutinho na Liverpool ko Eden Hazard na Chelsea ko kuma Dele Alli na Tottenham, kamar yadda jaridar Mirror ta ruwaito.
Dan wasan gaban Barcelona Andres Iniesta ya ce Neymar ne kawai ya san makomarsa, sai dai “ba na jin dan kwallon zai fi zama wa Barcelona alheri a kan a biyata Yuro miliyan 200 zuwa 300,” kamar yadda kafar yadaa labarai ta Marca ta bayyana.
Kungiyar Monaco ba ta son rabuwa da Thomas Lemar duk da cewa sau uku Arsenal ta yi zawarcinsa a kan Yuro miliyan 45, a labarin da Telegraph ta wallafa.
Daily Mail kuwa cewa ta yi Manchester City za ta bai wa dan kwallon Arsenal Alexis Sanchez albashin fan 320,000 a duk mako a kunshin yarjejeniyar ya buga mata tamaula.
Har ila yau, golan Manchester City Claudio Bravo wanda kasa guda suka fito da Sanchez wato Chile, ya ce za a karbi dan wasan hannu biyu-biyu idan ya koma City, kamar yadda Metro ta ruwaito.
Kungiyar West Ham za ta ki amincewa da duk wani tayi da Liverpool za ta yi wa Manuel Lanzini, a labarin da Evening Standard ta ce.
Daily Express ta ce Manchester United za ta tsawaita zaman Ander Herrera don ta dakile zawarcin da Barcelona ke son yi wa dan kwallon.
Liverpool ta dakatar da zawarcin da take yi wa dan wasan kungiyar RB Leipzig Naby Keita, amma za ta ci gaba da nemansa a kakar badi lokacin da take ganin kila Keita ya amince da tayin Yuro miliyan 48, kamar yadda jaridar Liverpool Echo ta bayyana.
Har ila yau, Express ta ruwaito cewa Arsenal tana zawarcin Jakub Jankto daga kungiyar Udinese ta kasar Italiya.
Har yanzu Manchester United na neman dan wasan Inter Milan Ivan Perisic in ji Independent.
Daga karshe dan kwallon Real Madrida, Gareth Bale zai bijirewa duk wani yunkuri na sayar da shi ga Manchester United, ya ce bai shirya barin Madrid ba, kamar yadda jaridar Daily Star ta wallafa.
Souce In Bbchausa
Add Comment