Jarumar Finafina Hausa, Hadiza Gabon Ta Yi Bikin Zagayowar Ranar Haihuwarta Tare Da Almajirai
Bikin wanda aka gudanar da shi a Kaduna, Jaruma Hadiza Gabon ta bayyana cewa ta yi hakan ne saboda akwai bukatar a daina barin marasa galihu a baya a duk wani shagulgula ko al’amuran ci gaba da ake samu.
A shekarar da ta gabata ma, Gabon ta yi biki makamancin haka ne tare da marayu.
Idan ba a manta ba dai, dab da za a soma Azumi jarumar ta rabawa makwabtan ta kayan abinci a unguwarsu dake Maidile a birnin Kano.
Allah Yasa Mudace
#Rariya
Add Comment