PDP ta yi watsi da sakamakon zaben jihar Kano

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta yi watsi da sakamakon zaben jihar Kano wanda hukumar zabe (INEC) ta ce Gwamna Abdullahi Ganduje ne ya lashe.

PDP ta zargi jam’iyyar APC da tilasta wa masu kada kuri’a da kuma tafka magudi musamman a mazabun da aka sake zabe a ranar Asabar.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 88

APC ta samu kuri’a 1,033,695, yayin da PDP ta samu jimilla 1,024,713. Hakan na nufin Ganduje ya lashe zaben ne da tazarar kuri’a 8,982.

A wani sako da PDP ta wallafa a shafinta na Twitter, jam’iyyar ta ce zaben Kano babban abin kunya ne.

Ta kuma zargi jami’an hukumar INEC da ta hadin baki da wasu ‘yan siyasa don bai wa dan takarar jam’iyyar APC kuri’a.

Zaben Kano dai ya ja hankali bayan sanar da da ba a kammala zaben ba a ranar Asabar 9 ga watan Fabrairu.

A zaben 9 ga watan Maris da aka gudanar PDP ce kan gaba da tazarar kuri’a sama da dubu 26.

An sake gudanar da zaben Kano ne a wasu mazabun kananan hukumomi 28.

Jam’iyyar APC ta lashe zaben a rumfunan kananan hukumomi 27 da aka sake zaben, yayin da PDP ta lashe karamar hukumar Dala.

Waiwaye

Rabi’u Musa Kwankwaso shi ne ubangidan Abba Kabir Yusuf a siyasance, kuma akwai takun saka sosai tsakaninsa da Gwamna Ganduje wanda a baya ya yi masa mataimakin gwamna har sau biyu.

A lokacin da PDP ta tsayar da Abba a matsayin dan takararta Kwankwaso ya sha suka a ciki da wajen jihar, inda ake zarginsa da cewa ya tsayar da surukinsa a matsayin dan takara.

Maimakon tsohon mataimakin Ganduje, Hafiz Abubukar da suka bata ya kuma koma wajen Kwankwaso.

Sai dai Kwankwason ya ce Abba ba mijin ‘yarsa ta cikinsa ba ne mijin ‘yar wansa ce, kuma bai tsayar da shi don radin kansa ba sai don ganin mutum ne da zai yi wa jihar Kano aiki bisa kishin kasa da jajircewa, sannan kuma “ba zai yi masa butulci ba.”

Yawan masu kada’a kuri’a a Kano

Kano dai ita ce ta biyu a yawan wadanda suka yi rijistar zabe a Najeriya bayan Legas, inda mutum miliyan 5,457,747 suka yi rijista amma mutum 4,696,747 daga ciki ne suka karbi katunansu na zabe.

Sannan kuma a jihar ba a samu raguwar masu kada kuri’a sosai ba idan aka kwatanta da na zaben shugaban kasa, ba kamar wasu jihohin ba da raguwar masu kada kuri’ar ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da na zaben shugaban kasar.

taswirar inecHakkin mallakar hotoINEC

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.