PDP Ta Bukaci A Dakatar Da Tattara Sakamakon Zaben Shugaban Kasa

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Jam’iyar PDP mai hammaya a Najeriya ta bukaci hukumar zabe INEC ta dakatar da tattara sakamako da take yi.

Jam’iyyar ta bukaci hakan ne har sai an nuna wa jam’iyyu yawan alkaluman da na’urar ta tantance jama’a a rumfunan da aka yi zabe.

Talla

A wata sanarwa da PDP ta fitar, ta yi zargin cewa an sauya alkaluman da na’urar tantance masu zabe ta nada tun farko domin yin magudi daga wasu jihohin da APC ke mulki.

Shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus ya ce sun mika bukatarsu ga shugaban hukumar zabe ta kasa.

Farfesa Mahnood Yakubu inda suke bukatar da soke zaben jihar Yobe da Nasarawa da Borno.

PDP ta kuma bukaci a sake zabe a jihohin.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 86

Tun da farko shafinsa na Twitter, Femi Fani-Kayode daya daga cikin manyan masu caccakar gwamnatin APC, ya yi kira ga dan takarar jam’iyyarsu ta PDP ya kafa gwamnati.

Fani-Kayode ya ce dole ne Atiku ya yi watsi da sakamakon da ake bayyanawa wadanda ya kira na jabu.

Ya ce idan har hakan ba ta samu ba zai kafa gwamnati.

Ya kuma ce suna da sahihin sakamako daga rumfunan zabe 119,000 da suka tabbatar da PDP ce ta yi nasara.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: