Pantami ya haramta wa kamfanoni tura sakon Voice Mail

3

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ministan Sadarwar Nigeria Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami ya haramta wa Kamfanonin sadarwar waya tura sakonnin Voicemail daga yau Al-hamis
Shi dai tsari na Voicemail wasu kamfanonin layukan waya ne suke yin sa, musamman Airtel suna sakawa mutum tsarin voicemail ba tare da amincewar sa ba, wannan hanya ce ta ha’inci da cuta da mugunta da damfarar ‘yan Nigeria.
.
Yadda abin yake shine; idan ka kira lambar waya musamman na Airtel sai ka tarar layin a kashe, ko user busy, mai makon a katse maka kiran, sai kawai a saka maka tsarin Voicemail wai ka fadi sakon da kake son isarwa ga wanda ka kira baka same shi ba, tsarin Voicemail din yana recording wai za’a tura ma wanda ka kira baka same shi ba, kuma Koda anyi recording din maganar ka baza a tura ma wanda ka kira din ba, an cuce an dauki kudin ka kawai.
.
Da zaran sun saka ka a wannan tsarin na Voicemail ba tare da amincewar ka ba sai su fara janye maka kudi, shine yanzu Ministan Sadarwa Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami ya haramta musu tsarin Voicemail, yace a soke shi gaba daya, domin ba karamin kudade ake tatsa daga jama’a ba a wannan tsarin, a sanina kamfanin layin Airtel ne ke da wannan tsarin na ha’inci da cuta da damfara

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.