Labarai

Osinbajo Ya Umarci Hafsoshin Soja Su Koma Maiduguri

Osinbajo Ya Umarci Hafsoshin Soja Su Koma Maiduguri

* Fiye Da Mutane 40 Boko Haram Suka Kashe A Jami’ar Maiduguri
_______¥_______

Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osibanjo ya umarci shugabannin rundunonin Sojan kasa, sama da na ruwa kan su gaggauta komawa birnin Maiduguri don sa ido kan yadda sojojin Nijeriya ke fafatawa da mayakan Boko Haram.

Ministan tsaro, Mansir Dan Ali ya ce Osbanjo ya kuma nemi a tanadi na’urorin hangen abokan gaba daga nesa don dakile duk wani harin ba- zata na Boko Haram Ministan ya nuna cewa ruwan sama na matukar kawo cikas kan kokarin da nasarorin d sojoji ke samu kan mayakan Boko Haram din.

A bangare daya kuma, Wasu wadanda suka ce sun shiga dakin ajiyar gawa na asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun ce mutum fiye da 40 ne suka mutu a harin da Boko Haram ta kai wa ma’aikatan aikin hakar mai a Magumeri, ranar Talata.

Ma fi yawancin mutanen da aka kashe din sojoji ne da ‘yan sintiri ko kuma kato da gora.
Tun da farko dai sojojin kasar sun ce sojojin tara suka mutu a kokarin ceto ma’aikatan wadanda da yawansu ma’aikatan jami’ar Maiduguri ne.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.