Labarai

Osinbajo Ya Sanya Hannu A Sabbin Dokoki Guda 7

Mukadashin shugaban kasar Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbanjo ya sanya hannu kan wasu sabbin dokoki guda 7 da suka tsallake karatu na uku a majalisa.
Mataimakin shugaban kasa na musamman a kan harkokin majalissu, Sanata Ita Enang ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Dokokin sun hada da dokar fansho da majalisa ta yi wa gyara, dokar tsaro wacce ta kunshi kirkiro da tauraron dan adam domin tsare harkokin yanar gizo a Nijeriya, da na tantance fina finai wanda ya kunshi bayarwa hukumar dama ta kula da shige da ficen fina finai cikin kasar, sai dokar hukumar kula da lafiyar dabbobi da sauran su.

Osinbajo dai shi ke rike da ragamar mulkin kasar tun bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi hutun kula da lafiyar shi a Birnin London ranar 19 ga watan Janairu.