Mukaddashin shugaban kasa, farfesa Yemi Osinbajo ya kai wata ziyarar bazata tashar jirgin sama na Murtala Muhammad da ke jahar Lagos.
Ya kai ziyarar ne domin ya duba halin da kayayyakin aikin tashar jirgin ke ciki, da kuma yadda ma’aikata ke gudanar da ayyukansu.
Wadanda suka yi rakiyar mukaddashin shugaban sun hada da karamin ministan sifirin jiragen sama Hadi Sirika da wani manaja a hukumar kula da tashoshin jiragen sama a Nijeriya (FAAN), Ephraim Nwodo.
Kayayyakin aikin da suka bincika sun hada da mashinan tantance matafiya, sashen duba visa, da sauransu.
Osinbajo ya nuna rashin jin dadinsa game da yanayin da ya samu wasu daga cikin kayayyakin aikin, inda ya ce akwai bukatar a inganta su cikin gaggawa.
Yayin da yake magana da manema labarai, Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya na yunkurin rage wahalhalun da suka jibanci gudanar da harkokin kasuwanci a kasar, kuma tashoshin jiragen sama na daya daga cikin bagarorin da suke dubawa wajen ganin hakan ta faru.
A fadarsa “mun duba kayayyakin aikin, kuma mun gani cewa wasu daga cikin su na bukatar canji, zamu yi iya kokarin mu wajen ganin an inganta su”



Add Comment