Labarai

Osinbajo Ya Fara Saka Da Mugun Zare

OSINGBAJO YA FARA SAKA DA MUGUN ZARE.

Daga Bashir Umar Malumfashi

Mukaddashin Shugaban Kasa Prof. Yemi Osinbajo ya Amince da nadin Manyan Sakatarorin Gwamnatin Tarayya guda 21,

Anyi wannan nadin ne domin cike gurabu 20 da aka samu saboda Dalilai daban-daban.

To saidai wadannan Nade-naden suna cike da Bangaranci da nuna banbanci addini da Kabila, bugu da kari sun sabawa tsarin Federal Charackter.

Nayi Imani da Shugaba Muhammad Buhari ne yayi Nade-nade irin wadannan ya cusa Al’ummar Musulmi da yawa kamar yadda Osinbajo ya cusa Kiristoci a wannan List, da yanzu hayaniya ta cika Jaridu da Kafofin yada labarai a Nigeria.

Akwai mamaki Gwamnatin da 85% zuwa 90% na Kuri’ar da taci Zabe mune muka Jefa ta, ace a wannan Gwamnatin ne ake rashin adalci haka.

1- Ehuria Ekeoma (Abia State).

2- Akpan Sunday (Akwa Ibom).

3- Anagbogu Nkiruka (Anambra).

4- Walson-Jack Esther (Bayelsa).

5-Gekpe Isu(Cross River).

6- Aliboh Lawrence (Delta)

7- Uwaifo Clement ( Edo).

8- Folayan Olaniyi (Ekiti state).

9- Osuji Marcellinus (Imo).

10- Adebiyi Adekunle, (Lagos).

11- Odewale Olajide (Ogun).

12- Adesola Olusade (Ondo State).

13- Adekunle Adeyemi,( Oyo state).

14- Nabasu Bako, (Plateau).

15- Ekaro Chukwumuebobo,( Rivers).

16-Aduda Tanimu from the Federal Capital Territory (FCT).

17- Mu’azu Abdulkadir (Kaduna).

18- Sulaiman Lawal (Kano).

19- Abdullahi Mashi (Katsina).

20- Ibrahim Musa Wen (Nasarawa).

21- Umar Bello (Sokoto).

Wato na fahinci mutanen nan da zarar sun sami dama duk yadda take basa wasa , za suyi anfani da ita su gina kansu.

2007 Mun samu ‘Yar’adua ya hau bayan shekara biyu Jonathan ya karba yayi shekara biyar da rabi yana Cutar damu.

2015 Allah ya taimake mu ya kawar mana da Jonathan, bayan shekara Biyu yanzu kuma mun sake fadawa wata Jarabawar, Allah ka agajemu, Allah ka bawa Muhammad Buhari lafiya.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.