Ministan wutar lantarki, gidaje da ayyuka na kasa Babatunde Raji Fashola a wata taron FEC na Majalisar zartarwa ta tarayya a jiya a Abuja wanda Osibanjo ya jagoranta, ya bayyana cewa Mukkadashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo ya saki wasu kudade na manyan kwangiloli.
Gwamnatin tarayya ta bada kwangilar ginin titin kan iyaka tsakanin Nijeriya da kasar kamaru wanda zai ci makudan kudi har Dala miliyan 38, da dama dai can an yi rabin aikin a baya.
Haka zalika Gwamnatin Nijeriya za ta gina wani titi a gabashin Kaduna mai kilomita 15 dauke da gadoji saboda ruwa wanda zai ci sama da Naira biliyan 30, kwangilar da aka bayar tun shekarar 2002 amma har yau an kasa samun ci gaba.
Add Comment