A yayin da Yarbawa ke ci gaba da matsim lamba kan batun sakewa Nijeriya fasali, Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegum Obasonjo ya nesanta kansa daga masu wannan kiraye kirayen inda ya nuna cewa mutane ne ya kamata su canja halayensu.
Ya kara da cewa abin da ya kamata al’ummar Nijeriya su fifita shi ne yadda za a sarrafa arzikin kasa ta yadda kowa zai amfana.
A cewarsa, ya zauna da kusan mutane shida masu ra’ayin sakewa Nijeriya fasali amma sai ya fahinci kowa na da tasa manufa.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar na daga cikin wadanda ke kan gaba wajen neman a sakewa Nijeriya fasali, ra’ayin da Shugaba Buhari ya fatali da shi.
Souce In Rariya
Add Comment