Get New DJ Mixes
Nasiha

[Nsiha] GYARAN ZAMAN AURE

GYARAN ZAMAN AURE

1-Matsalar Farko- BAYA SHIGOWA GIDA DA WURI:
Yaya yake fita daga gidanki?Idan ya fita wane sako ki ke aika masa?Ya kike karbarsa idan ya dawo?Ya yake samunki?Ya yanayin gidan ki ya ke?Ya makwancisa ya ke?

2-Matsala Ta biyu- BAYA CIN ABINCINA:
Yaya tsaftar wajen girkin ki?Yaya kike shiga kicin? (Tsaftarki)Yaya kike hada girkinki?Me ya fi so a dafa masa?Wadanne irin kwanuka kike amfani da su wajen zuba abincinsa?Yaya wajen da zai ci abinci yake?Ya kike shiryo masa kayan abincinsa da zai ci?Ya kike karbarsa lokacin da ya zo cin abincinsa?

2-Matsala Ta Uku – YANA DAURE FUSKA:
A wane hali ya fita daga gidan?Yaya yana yin aikin sa yake?Da su wa yake harka idan ya fita?Ya yanayin samunsa yake?Idan ya daure fuska, ke ya kike masa?

4-Matsala Ta Hudu – BAI DAMU DA NI BA:
Kin sauke masa nauyin da Allah ya dora miki na sa a matsayin sa na mijinki?Kina kula da abin da yake so? Da wanda ba ya so?
Kina jin damuwarsa a ranki? Ya kike tafiyar da shi?
Ya kina masa wasa ?Ya kina nuna masa kula da mahaifansa da danginsa ?Ya kina masa addu’ah ?

5-Matsala Ta Biyar – BAYA KULA DA YARA:

Yaya tarbiyyar yaran?
Yaya tsaftarsu?Ya suka dauki mahifinsu?Da wa yaran suke harka?

6-Matsala Ta Shida – YANA FITA YA BAR NI DA SASSAFE:

Wane irin karba ya samu da daddare?Bayan tashinsa daga bacci ya kika karbe shi?Ya yanayin gidan yake?

7-Matsala Ta Bawai – IDAN NA YI BAKI YANA JIN HAUSHI:

Yayin da kike da bakin wane irin kulawa kike ba wa mijinki?Kin fifita bakinki a kansa?Kina fifita ‘yan’uwanki a kan nasa?Wane irin baki kike yi?

8-Matsala Ta Takwas – BA YA YABA KWALLIYATA:

Wacce irin kwalliya mijinki ya ke so?Yaya kike tsara kwalliyarki?Yaushe kike kwalliyar?

9-Matsala Ta Tara – BA YA HIRA DA NI:

Ya kike hirar?Kin iya hirar ma kuwa?Wane lokaci kike zuwa hirar?

10’Matsala ta Goma – BAYA BARI NA FITA KOMAI MUHIMMANCINTA
:Ya kike fitar?Yaushe kike fita da dawo wa?Kina sauke nauyin da ke kanki kafin ki fita?Kin iya tambayar fitar?

11-Matsala Ta Sha-Daya: YA CIKA FADA.Me yake sa shi fadar?Yaushe yake fada?A kan me yake fada?In yana fadan ya kike?

12-Matsala Ta Sha-Biyu – YANA KULA MATA A WAJE:

Son yin hirar da su ne da shi?Ko daukarsu yake su kebe?Me yake so a jikin mace?Shin kina kyautata masa abin da yake so a jikin mata?Ko a hoto, me kike ganin ya fi sha’awa a jikin mace?Kina yi masa hakan?

13-Matsala Ta Sha-Uku – YA KI BARI NA IN SAKE DA MAKWABTANAWadanne irin makwabtab kike da su?Ya yake kanki ki ke?Yaya mu’amalar makwabtan na ki.

 Wannan sako ne daga Dr Jilani Almustapha Danmalam kano.

Tsarawa da Yadawa:
Mustapha Musa abu Aisha.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.