-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Furudusoshi Sun Daina Sakani A Film Shiyasa Nadawo Siyar Da Kunun Aya, Inji Chiroki


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shafin sada zumunta na Instagram na Northern_hibiscuss ya tara wa Bashir Bala Ciroki kudi fiye da naira 200,000 a ranar Talata.

An fara tara wa daya daga cikin `yan wasan farko da suka shahara a masana’antar fina-finan Hausa ne bayan da aka samun labarin cewa yana tallan kunin aya.

A wata hira da gidan talbijin na Arewa 24 , Ciroki ya yi ikirarin cewa masu shirya fina-finai da jaruman Kannywood sun daina sanya shi a fim, shi ya sa a yanzu yake sayar da kunun aya.

Jarumin fina-finan Kannywood Ali Nuhu ya kalubalanci wani mai amfani da shafin Twitter cewa ya bayyana masa mutanen da abokin sana’arsa Bashir Bala, wanda aka fi sani da Chiroki, ya tallafa wa lokacin da tauraruwarsa ke haske a fagen wasan kwaikwayo.

Shi dai mutumin, wanda ke amfani da sunan Doctor Kiyawa, ya nuna rashin jin dadinsa ne kan yadda ya ce jaruman Kannywood sun yi watsi da Chiroki duk da cewa yana bukatar taimako.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 331

- Advertisement -

Doctor Kiyawa ya yi zargin cewa mata kan shiga harkar fim cikin shekara guda su yi kudi amma mazan da suka kwashe shekara da shekaru suna harkar ba sa samun komai

“a Kannywood ne za ka ga mace ta shigo fim wannan shekarar amma ta fi wadda ya yi shekara 10 yana sana’ar fim kudi. Ali Nuhu, kai ne wadda yanzu jama’a suke gani da kima a Kannywood, don Allah ku yi wa [Chiroki] wani abu wanda shi ma ba zai manta cewa kun yi masa halacci ba.”

Sai dai a jerin martanin da Ali Nuhu ya yi wa masu irin wannan korafi, ya kalubalance su da su nuna masa irin taimakon da Cirokin ya bai wa Kannywood.

“Zan yi maka tambaya: lokacin da Ciroki yake tashe wa ya taimaka wa? Maimakon haka, a kan kudi mene ne ba ya yi wa masu shirya fim? Ya kamata mu san abin da muke yi.”

Ya ce bai kamata a rika yi wa ‘yan Kannywood rashin adalci ba, wajen dora alhakin gazawar wani daga cikinsu a kansu.

Jarumin ya ce babu wani da ke Kannywood da zai taimaka wa Ciroki, yana mai cewa “ya kamata ya dawo masana’antar ya sasanta da masu shirya fina-finai, sannan ya ci gaba da aiki kawai.”

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: