Labarai

Nnamdi Kanu Ya Zama Babbar Barazana Ga Jami'an Tsaron Kasar Nan

Daga AbdulRa’uf Matawalle (Sarkin Yakin Baba Buhari)
Wanna babban barazana ce da kalubale ga hukumomin tsaro ta kasata, mahaifata Nijeriya.
Wannan shine Bahaushe ke cewa ba a rabu da Bukar ba, an haifi Habu.
Manufa ta a nan shine Gwamnati tarayya tana kokarin kawar da kungiyan shedanu na Boko Haram wata kuma tana kunno kai, wadda bisa alamu suma wa da kani ne.
 
Wanda a ranar 27/8/2017 suka gudanar da babban taron su a birnin Aba dake jihar Abia. A inda jagoran tsagerun Biafaran ke furta barazanan kashe duk wani jami’in tsaron Nijeriya da ya yi kokarin kamo shi ko hana shi kafa kasar Biafara. Inda ya ce ko SSS ko soja ko dan sanda.
Amma abin tambaya anan shine wai a jihar Abia babu gwamna ne? A jihar Abia babu ‘yan sanda ne da dai sauran hukumomin tsaron koko suma sun zama Biafara ne?
Kuma abin da talakan Nijeriya ya kamata ya duba a Gwamnatin adali Baba Buhari ana fuskantar barazana wadda hakan ya jawo biliyoyin kudin kasar ke salwanta.
Wanda a Gwamnatin baya su ‘yan Biyafara ba su fito ba.
Saboda haka ina kira ga Gwamnati da ta zamo ba sani ba sabo don ganin ta tabbatar da tsaro ga al’umman Nijeriya.
Allah ya kara wa shugaban kasa lafiya, ya ba mu lafiya da zama lafiya a kasar mu Nijeriya. Amin.