Malam Garba Shehu, Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin watsa labarai, ya bayyana cewa Nijeriya ce ta biyu a noman shinkafa a fadin duniya. Ya bayyana haka ne a yayin da ya halarci wani taro na musaman na matasa a karkashin tsarin wata hukuma mai suna “Citizen Supports for Good Governance”(SGGN) a Abuja
Ya ce” Babu wata kasa da za ta samu cigaba in har za ta cigaba da siyen kusan komai daga kasashen waje, kusan duk abincin da muke ci a Nijeriya ana shigo da su ne daga kasashen ketare saboda haka dukkan kudaden da kasar ke tarawa suna tafiya a harkar shigo da abinci ne
Amma a yanzu Nijeriya dai ta samu nasarar zama kasa ta biyu a noman shinkafa a duniya, hakan ya samo asali ne daga juyin juya hali da kasar ta yi a noman shinkafa a shekaran da ta gabata, wani gidan jarida ya yi bincike a jihar kebbi suka gano cewa akalla mutane 48,000 a jihar Kebbi suka yi arziki da noman shinkafa

“Dogaro da arzikin mai ya gurgunta arzikin kasar kuma hakan ba zai taimaka wa kasar ba. Sarrafa tattali arzikin kasar zai rage talauci kuma ya kawo cigaba a kasa baki daya
“This over-reliance on oil has killed this country and we cannot continue like this. So, the diversification of the economy means more money will be in the hands of ordinary Nigerians. And there will be widespread prosperity all over the country
Add Comment