Labarai

Nigeria: Me ya sa mata suka fi shan kayan maye a Kano?

A Najeriya, mahukunta a jihar Kano arewacin kasar na kuka da yadda matsalar shan kayan maye ke karuwa a tsakanin al`umma.

A baya dai samari ne aka sani da gudanar da irin wannan tabi’u na ‘ammali da kayen maye.

To amma lamarin yanzu ya kusa zama kusan ruwan dare a tsakanin mata da ‘yanmata a arewacin Nijeriya.

In ji hukumomin dai matan aure da `yan matada ke ta`ammali da kayan mayen, na hadawa da wasu magungunan mura da na cututtuka da akan samu a kananan shagunan sayar da magani.

Alhaji Hamza Umar babban kwamandan hukumar da ke yaki da shan miyagu kwayoyi na jihar Kano ya ce abin ya yi matukar yawa a jihar Kano, wanda matsalar ta fi yawa a tsakanin matan aure, da zawarawa, da kananan ‘yanmata, da ko biki ake sai sun tanade su.

 

Galibi dai abokai ne ko kawaye ne ke koya wa junansu shaye-shayen kwayoyin.

Babban kalubalen da ake fuskanta a yaki da wannna dabi’a shine yadda masu shan kayan mayen ke samun kayan hadin cikin sauki.

Masana dai sun ce idan ba a gagguta daukar matakin dakile wannan dabi`a ba, to a karshe za a samar da wata al`uma marar kan-gado.

A halin da ake ciki dai rundunar hukumar da ke yaki da miyagun kwayoyi ta jihar Kanon ta kafa wani kwamiti don wayar da kan jama`a a kan wannan matsalar.

Aikin da hukumar da ke yaki da miyagun kwayoyi a jihar kadai ba ya isa wajen warware bakin zaren sai an hada da shugabannin addinai daban-daban.

 

Souce IN BBCHAUSA

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.