Labarai

Nigeria: Wane shiri filin jirgin saman Kaduna ya yi?

Hukumomi sun ce a shirye filin jirgin saman Kaduna yake ya dauki jiragen da suke sauka a Abuja
An fara aiki a filin jirgin saman Kaduna da ke arewacin Najeriya domin shirye-shiryen da ake yi na komawar jiragen da ke sauka da tashi a filin jirgin saman Abuja, babban birnin kasar, sauka a Kadunar.
A ranar Alhamis ne dai ake sa ran jirage za su fara sauka da tashi daga filin jirgin na Kaduna kuma har tsawon makonni shida sakamakon gyare-gyare da ake yi a filin jirgin saman na Abuja.
Jami’in a hukumar kula da sufurin jiragen sama a Najeriya (FAAN), ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ma’aikatar na aiki domin aiwatar da duk wasu gyare-gyare a filin jirgin saman.
Sai dai kuma rahotanni dai na cewa an gyara wasu bangarorin ginin tare da wasu na’urori amma ba a gyara kayayyakin wutar lantarki ba, da kujerun zama da wuararen ajiyar motoci wadanda suka lalace.
An dai ambato kamfanonin jiragen sama da dama na cewa ba za su sauka a filin jirgin saman na Kaduna ba saboda babu tabbacin tsaron lafiyar fasinjojisu a yankin.
Satar mutane dai domin neman fansa ta yi kamari a jihar Kaduna.
AbujaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Wata jami’a a hukumar kula da sufurin jiragen sama a Najeriya ,Henrietta Yakubu ta bayyana wa BBC cewa shirye-shirye sun yi nisa wajen daukar matakan kare lafiyar fasinjoji.
Jami’ar dai ta ce matakan da suka dauka sun hada da amfani da bas-bas da kuma ‘yan sanda.
Kamfanin jirgin sama na British Airline da Lufthansa da dai sauransu sun ki amincewa su sauka a Kadunar sabanin na Habasha da ya yarda ya sauka a Kaduna.
Wani jami’i daga hukumar FAAN ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na Reuters cewa an aika ‘yan sanda zuwa yankin, domin tabbatar da harkokin tsaro sannan kuma an gyara hanyoyin mota.
Filin jirgin saman Kaduna na iya daukar fasinjoji 500 a lokaci guda.
Birnin Kaduna dai na da tazarar kilomita 190 daga Abuja, babban birnin kasar.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.