An samu hatsaniya a sakatariyar ‘yan jarida da ke jihar Kaduna yayin da wasu sanatocin jam’iyyar APC ke taro da manema labarai, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
“Wadansu mutane ne dauke da makamai suka kai hari cibiyar ‘yan jarida da ke kan hanyar Muhammadu Buhari Way (Waff Road) ranar Lahadi,” a cewar rahotanni.
Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hukunyi da kuma wasu ‘yan siyasa jihar ne suka kira taron manema labaran.
“Yau (Lahadi) a sakatariyar ‘yan jarida da ke Kaduna muna cikin taro da ‘yan jarida kan yadda za mu kaucewa yunkurin gwamnatin jihar na karbe jam’iyyar (APC) da kuma rusa ta,” kamar yaddda Sanata Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na Facebook.
“Sai wasu ‘yan daba suka far mana da taimakon ‘yan sanda, inda suka lalata motocinmu suka kuma kai wa wasu mutane da ba su ji ba, ba su gani ba hari,” in ji shi.
Kodayake rahotanni sun ce ba a samu asarar rayuka ba, amma wani dan jarida ya jikkata.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufa’i ya yi Allah-wadai da al’amarin a wani sako da ya aike wa kungiyar ‘yan jarida reshen jihar ta hannun mai taimaka masa kan kafofin yada labarai, Samuel Aruwan.
Ya ce ya umarci a fara bincike kan al’amarin da ya faru, “kuma na aike da karin jami’an tsaro sakatariyar don tabbatar da tsaro.”
An dade ana samun takun saka tsakanin bangarorin jam’iyyar APC biyu a jihar wato ‘yan APC akida da kuma maso goyon bayan gwamnatin jihar.
‘Yan APC akida suna zargin gwamnatin jihar da kin cika alkawuran da ta daukar wa jama’a, yayin daya bangaren kuma yake musanta zargin.
Dan jaridar da ya ji rauni yayin hatsaniyar
Wani gilas din kofa da aka fasa
Wata mota da aka fasa gilashinta
Souce In Bbchausa
Add Comment