Labarai

Nigeria: Shugaba Buhari na kan hanyar komawa gida yau Asabar

Buhari dai ya shafe fiye da kwana wata uku a Landan

Fadar Shugaban Najeriya ta ce nan gaba a yau Asabar ne ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai koma gida bayan wata doguwar jinya a birnin Landan.

A cikin wata sanarwa da Mai bai wa shugaban Shawara kan watsa labarai Femi Adesina ya fitar ya ce ana sa ran shugaban ya yi wa ‘yan kasar jawabi ta gidajen radiyo da tallabijin ranar Litinin da safe.

”Ya gode wa daukacin ‘yan Nigeria wadanda suka yi ta yi masa addu’ar samun lafiya da fatan alheri tun lokacin da ya fara kwantawa ciwo,” inji takaitacciyar sanarwar mai sakin layi hudu.

Shugaba Buhari dai ya bar kasar ne ranar 7 ga watan Mayu domin jinyar rashin lafiyar da ba a bayyana ba; bayan ya mika ragwamar shugabancin kasar ga mataimakinsa wanda ya kasance mukaddashin shugaban kasar tun sannan.

Wannan dai shi ne lokaci mafi tsawo da wani shugaban kasar ya taba kwashewa yana jinya a kasar waje kuma dawowar tasa na zuwa ne ‘yan kwanakki bayan da wasu ‘yan kasar suka fara zanga-zanga suna kiran ya dawo ko yayi murabus.

 

Bbchausa