Labarai

Nigeria: An saki wanda ya sanya wa karensa suna Buhari

Fadar shugaban kasa ta ce Shugaba Buhari ya mayar da batun abin dariya

A Najeriya, hukumomi sun kori wata kara da aka shigar ana tuhumar wani mutum mai shekara 41, wanda ya sanya wa karen sa sunan Shugaba Muhammadu Buhari.

 

An kama Joachim Iroko, wani dan kasuwa da ake cewa Joe Fortemose Chinakwe, a shekarar 2016, bisa zargin sa da neman tayar da rikici a kasar.

Wani alkali a jihar Ogun da ke kudu maso yammacin kasar ne ya yi watsi da karar, inda ya ce masu shigar da karar ba su bayar da kwakkwarar hujja a kansa ba.

Tsare Mista Iroko da aka yi ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar, inda masu suka suka zargi jami’an ‘yan sanda da take hakkin mutum na walwala.

A lokacin dai, mai magana da yawun shugaban Najeriya Garba Shehu, ya ce ya tabbata shugaban na can ya mayar da lamarin abin dariya, ganin yadda duk wanda ya alakanta shi da lamarin to yana nuna jahilcinsa ne kawai a fili.

 

Bbchausa