Labarai

Nigeria: ‘Muna goyon bayan Buhari ko zai shekara a London’

A ranar Lahadi ne Shugaba Buhari yana da wasu gawmnonin jam’iyyar APC a Landan

‘Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu tun bayan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wasu gawmnonin kasar a Landan inda yake jinya.

A muhawarar da aka tafka a shafukan sada zumunta na BBC Hausa Facebook da kuma Twitter mutane da dama sun bayyana ra’ayoyinsu.

 

Ga kadan daga cikinsu:

M Baban Yusurah Gusau cewa ya yi: “Samun labarin murmurewar Shugaba Muhammadu Buhari daga bakin gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, wani babban abin farin ciki ne, AllahYa kara mashi lafiya da sauran marasa lafiya na duniya baki daya.

Nuraddeen Ashiru Mani: Tabbas, mu talakawan Najeriya mun yi murnar samun labarin Shugaba Buhari yana samun sauki har ma kuma ya gana da tawagar gwamnoni a Landan, wannan kuma zai zama kalubale ga masu shaci fadi game da rashin lafiyar shugaban”.

Sai dai Rukaiyya Usman Fari Jebuwa ita ta bukaci karin haske ne game da shugaban da kuma lokacin da zai dawo.

“To fadar gwamnatin taraiyar Najeriya yakamata ki bayyanawa al’ummar kasar dangane da halin da Shugaba Muhammadu Buhari yake ciki don sanin ko yaushe zai dawo gida,” in ji ta.

Murtala Ibrahim Zangon Daura kara nunawa goyon bayansa ga shugaban ya yi: “Ko shekara guda Buhari zai yi a birnin Landan, talaka yana tare da shi wajen yi masa addu’ar samun lafiya,” in ji shi.

Sai dai kuma akwai wadanda suka nuna rashin amincewarsu da halin da gwamnonin suka ce sun gani na ci gaba tattareda shugaban kasar.

Nuhu Guzalla shakku ya nuna game da kalaman Gwamna Rochas.

Duk yaudara ce. Rochas ka ji tsoron Allah ka yi bayani gaskiya kan rashin lafiyar Buhari don babu wanda ya fi karfin rashin lafiya a duniya. Tambayata kawai ita ce me yake damun Buhari? Me ya sa Buhari baya so yayi hira da ‘yan jarida tunda yana samu lafiya?,” in ji shi.

Suleiman Lawal Giwa cewa ya yi:”Ya kamata a sanar da ‘yan kasa ranar da Shugaba Muhmadu Buhari zai dawo, domin ci gaba da aikinsa.”

Har ila yau, akwai wadanda suka bayyana jin dadinsu game da ganin shugaban a karon farko cikin fiye da wata biyu.

“Masha Allah, Farin ciki ya lullubeni zuciyata bayan na ga hoton Buhari tare da gwamnoni,” in jiAuwal Salihu.

Abbas Yusuf cewa ya yi: “Allah Ya karawa Buhari lafiya da tsawon kwana da hikiman gudanar da mulki da yin adalci ga talakawa, ameen.


Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017

19 ga watan Jan – Ya tafi Birtaniya domin “hutun jinya”

5 ga watan Fabrairu – ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya

10 ga watan Maris – Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba

26 ga watan Afrilu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma “yana aiki daga gida”

28 ga watan Afrilu – Bai halarci Sallar Juma’a ba

3 ga watan Mayu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku

5 ga watan Mayu – Ya halarci sallar Juma’a a karon farko cikin mako biyu

7 ga watan Mayu – Ya koma Birtaniya domin jinya

25 ga watan Yuni – Ya aikowa ‘yan Najeriya sakon murya

11 ga watan Yuli – Osinbajo ya gana da shi a Landan

23 ga watan Yuli – Ya gana da wasu gwamnoni a Landan

 

Bbchausa

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.