Labarai

Nigeria: Matasa sun kai harin ramuwar-gayya kan ofishin MTN

Wasu masu zanga-zanga a Najeriya sun kai wa ofishin kamfanin wayar sadarwa na MTN hari a Abuja, babban birnin kasar.
Masu zanga-zangar sun kai hari ne don nuna fushinsu a kan hare-haren kin jinin baki da aka kai wa baki da suka hada da ‘yan Najeriya a Afirka ta Kudu.
Duk da cewa ba su samu damar kutsawa cikin ofishin ba, amma sun farfasa gilasan tagogi, tare da lalata allunan tallan kamfanin da ke kafe a kofar shiga.

An yi ta fita da ma’aikatan kamfanin, wanda mallakar Afirka ta Kudu ne, ta kofar baya saboda gudun kada abin ya rutsa da su.
Zuwa yanzu dai ba a kama ko mutum guda ba daga cikin masu zanga-zangar.
Kamfanin MTN din ya fitar da sanarwa, inda yake nuna matukar damuwarsa a kan tashe-tashen hankulan da ke faruwa faruwa a kasashen biyu.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito kakakin kamfanin na cewa, “Suna zanga-zangar ne kan abin da ya faru na kai wa baki hari a Afirka ta Kudu. Wannan shi ne babban ofishinmu na yankin Yammacin Afirka.”
Ya kara da cewa, “A nan ne muke hulda da abokan cinikinmu. Sun lalata mana kayan aiki, sun sace wayoyin abokan ciniki, sannan sun far wa wasu daga cikin su.”

Ofishin MTN a Abuja, Nigeria
Image captionJami’an tsaro ne ke gadin ofishin a halin yanzu

Rahotanni sun ce daga ofishin MTN, masu zanga-zangar sun wuce ne zuwa kamfanin tauraron dan adam na DSTV a Abujar, wanda shi ma mallakar ‘yan Afirka ta Kudu ne.
Ya kuma bukaci mutane da su kwantar da hankalinsu.
‘Sanadin harin’
A wannan makon ne aka kona shaguna kusan 30 na ‘yan ci rani a Pretoria babban birnin Afirka ta Kudu, duk da cewa ‘yan sandan kasar sun ce ba baki aka yi niyyar kai wa harin ba.
Da ma dai gabannin kona shagunan, mai bai wa shugaban Najeriya shawara a kan ‘yan kasar mazauna wasu kasashen Abike Dabiri, ta yi kira ga Afirka ta Kudu da kungiyar Tarayyar Afirka da su yi kokarin kawo karshen hare-haren kin jinin bakin.

A ranar Talata ma matasa sun yi wata zanga-zangar a AbujaHakkin mallakar hotoA RANAR TALATA MA MATASA SUN YI WATA ZANGA-ZANGAR
Image captionA ranar Talata ma matasa sun yi wata zanga-zangar a Abuja

Amma sai gwamnatin Afirka ta Kudun ta yi fatali da kiran tana mai musanta cewa an kai wa ‘yan Najeriyar harin.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da ake samun matsalar kai hare-haren kin jinin baki ba.
Ko a shekarar 2015 ma an samu irin wadannan hare-hare a Afirka ta Kudu, inda aka kashe mutane tare da kona wuraren sana’arsu, da suka hada da na ‘yan Najeiya.
Hakan tasa a ka yi zanga-zanga a Najeriyar a gaban ofisoshin jakadancin Afirka ta Kudu da kamfanin MTN.