Malaman jami’o’in gwamnati a Najeriya sun fara wani yajin aikin sai baba ta gani daga Lahadi 13 ga watan Agusta.
Malaman sun bayyana wannan matakin nasu ne bayan taron kungiyarsu ta malaman jami’ar Najeriya, ASUU, da safiyar Litinin.
A wajen taron, shugaban kungiyar ASUU, Biodon Ogunyemi ya bayyana dalilansu na dugunzuma yajin aikin.
Malaman na neman a biya musu wasu bukatu da suka hada da al’amuran jin dadin malamai, da karin kudaden gudanarwa domin inganta yanayin ilimi a jami’o’in.
Kungiyar ta ASUU ta ce malamai da dama daga jami’o’in dake wasu sassan kasar basa samun cikakken albashinsu.
Tun watan Nuwambar 2016 gwamnatin tarayyar Najeriya ke tattaunawa game da wadannan bukatun na kungiyar malaman jami’a.
A cikin bukatun da kungiyar ASUUn ta gabatar, har da kira ga gwamnati ta tabbatar da an sako wasu malaman jam’ar Maiduguri da kungiyar Boko Haram ta ke garkuwa da su.
Wannan batu na yajin aikin ya ja hankalin ma’abota shafukan sada zumunta, inda suka yi ta tafka mahawara game da dalilai da tasirin wannan matakin.
Mista Ogunyemi ya ce yajin aikin zai shafi dukkan jami’o’in gwamnatin Najeriya dake ko ina a fadin kasar.
“A lokacin wannan yajin aikin, zamu daina koyarwa, kuma babu shirya jarabawa da halartar tarurruka a dukkan rassanmu”, inji shi.
Add Comment